LAFIYA JARI

 • LAFIYA JARI

  Posted by Umar Ibrahim on August 10, 2021 at 8:38 am

  Assalamu alaikum

  Za mu yi magana ne insha Allahu a kan magungunan gyambon ciki, majinar ciki, kumburin ciki, da sauran su. Matsalolin basur da Olsa (gyambon ciki) da majinar ciki da kumburin ciki, kusan sun mamaye ko’ina a cikin ƙasashen mu.

  Mu dai a nan arewacin Nigeria kusan kashi 70 na Jama’a za ka iske suna fama da ɗaya ko biyu daga cikin abubuwan da aka lissafo ɗinnan. Don haka ne muka ƙuduri aniyar binciko ma al’ummah hanyoyin magance waɗannan matsalolin ta hanyar amfani da Likitancin addinin Musulunci.

  1. JAN TUMATUR : Wasu daga cikin likitocin musulunci bincikensu ya tabbatar da cewa duk mutumin da ke fama da matsalar gyambon ciki, idan yana shan jan tumatur guda uku kullum da safe kafin ya ci komai, zai samu sauƙi sosai. Kuma zai daina yi masa mummunan tashin nan da yake yi.

  Haka nan shan Jan tumatur guda uku a kullum da safe zai yi amfani sosai ga mutumin da ke fama da ciwon Sikila (sickle cell anemia) da kuma masu fama da ciwon Zuciya insha Allahu. Domin tumatur yana buɗe hanyoyin jini, yana samar da manyan sinadarai irin waɗanda jiki ke buƙata.

  NOTE : Idan za a sha a nemi wanda ya nuna, kuma ban da ruɓaɓɓe.

  2. KABEWA : A samu kabewa a yanka ta a dafa. Sannan a ɗebi ruwanta kofi guda a haɗa da Madara ko Nono, a zuba suga sannan a riƙa sha da ɗumi-ɗuminsa har na tsawon kwana 7.

  Wannan insha Allahu zai magance matsalar Olsa ko kumburin ciki. Kuma zai magance matsalar mutuwar mazakuta ga mazaje. Da kuma matsalar bushewar ni’ima ga mata.

  Namijin da ba ya haihuwa ta sanadiyyar ƙarancin ƴaƴan Maniyyi (Low Sperm count) shi ma idan yana shan wannan za a dace. Amma shi zai rinƙa sha da nonon Rakumi ne, amma wanda bai fara lalacewa ba.

  3. FUREN ALBABUNAJ : A samu furen Albabunaj na ainihi (me kyau ɗin) a niƙa shi, a samu kamar cikin cokali 7 na garinsa. A haɗa da garin Habbatus-sauda cokali 7, sannan a riƙa ɗibar cokali guda da rabi ana dafawa da ruwa kofi guda.

  Idan ya dahu sai a tace sannan a sha haka, ko kuma da zuma. Insha Allahu zai magance matsalar Basur, Kumburin ciki, da Olsa.

  Masu fama da ciwon ƙoda koda ta kumbura insha Allahu za ta sace. (za a sha har sati 6).

  Masu fama da matsalar rashin barci, idan suna sha za su samu barci sosai. Haka nan mai fama da natsalar rikicewar ƙwaƙwalwa idan ya sha zai samu sauƙi.

  Matar da take fama da matsalar rikicin jinin Haila ko toshewar Mahaifa idan tana sha za ta warke insha Allahu.

  4. ƁAWON AYABA : A samu ɓawon ayaba ko Plantain a shanya a inuwa sannan a daka shi bayan ya bushe. A samu kamar garinsa cikin cokali 7.

  A riƙa zuba cokali guda na wannan garin a cikin Madara rabin Gwangwani a sanya zuma mai kyau sannan a sha.

  Za a maimaita har tsawon kwanaki 10 ko 14. Ana sha kullum safe da yamma.

  Insha Allahu za a warke daga Olsa, za a samu ƙarfin kuzari ga Namiji, Mace ma za ta samu ni’ima a jikinta. Sannan za a samu waraka daga ƙugi ko rikicin ciki. Insha Allah.

  5. ƁAWON RUMMAN : A samu ɓawon rumman a daka shi sannan a gauraya da zuma tare da garin ƙwallon Kankana (daidai rabin wancan). Za a sha har tsawon Wata guda.

  In sha Allahu za a samu waraka daga cutar gyambon ciki, Ɗaukewar sha’awa, Dattin ciki, Majinar Ciki, da sauransu.

  6. MAN HABBATUS SAUDA : Cokali guda na man Habbatus-sauda, Cokali uku na Zuma, Cokali guda na garin ‘ɓawon rumman, a hada su waje guda a sha.

  Bayan an sha sai kuma a sha kofi guda na Nono (tsala ko Kindirmo) ko kuma Madara gwangwani guda. Insha Allahu za a samu lafiya daga cutar Olsa, Basur, da kuma ciwon Hanta.

  7. GARIN TAFARNUWA : Garin tafarnuwa cokali goma, Garin Habbatus sauda cokali goma. A hada su da zuma a riƙa shan cokali guda da safe kafin karyawa. Sannan cokali guda duk bayan awa uku Har zuwa dare.

  Insha Allahu za a samu waraka daga ciwon Olsa, sanyin Ƙirji (Pneumonia) da kuma cushewar ciki.

  8. FUREN BANAFSAJ : Idan ana dafawa ana shansa yana magance ciwon daji, Olsa, da sauransu.

  9. DANKALI : A samu dankali ‘ ɗan hausa (Sweet Potatoes) a niƙa shi a blender sannan a ɗebi kofi biyu na ruwansa a sha. Sannan bayan awa daya da rabi a sha ruwan Shammar.

  Insha Allahu za a samu waraka daga cutar Olsa, daji, da sauransu.

  ABIN LURA: Koda ana amfani da wani daga cikin wadannan laƙanin, to wajibi ne a kiyaye daga abubuwan da ke kawo motsawar jinya ga masu fama da Olsa ko kumburin ciki ko basur. Misali kamar :

  – Dole ne a daina ci ko shan abubuwa masu tsami, Ko masu kaushi, ko masu tsananin sanyi ko zafi.

  – Dole ne a daina daɗewa cikin yunwa.

  – A daina kwanciya da zarar an ci abinci har sai bayan an motsa jiki, ko kuma a jira kamar minti 30.

  (An samo daga ZAUREN FIQH whatsapp group 2)

  Magaji Mohammed replied 1 year, 5 months ago 2 Members · 1 Reply
 • 1 Reply
 • Magaji Mohammed

  Organizer
  August 17, 2021 at 3:28 pm

  Masha Allah. Allah Ya kawo mana sauki. Ameen.